Posts

Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Babbbar Matatar Mai Ta Dangote A Lagos

Image
Shugaba Muhammadu Buhari Zai Kaddamar Da Babbar Matatar Mai Ta Dangote A Legas Ana sa ran fara aikin wannan matatar Mai zai haifar da gagarumin tasiri ga tattalin arzikin Najeriya da kuma rayuwar 'yan kasar. A halin yanzu dai Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke da arzikin Man Fetur a nahiyar Afirka, amma duk da haka ta dogara kacokan kan shigo da taceccen mai daga kasashen waje domin biyan bukatunta na cikin gida. Kasar dai na kokawa da kalubalen rashin isassun kayan aikin tace mai a cikin gida, lamarin da ya janyo raguwar kudaden da take samu daga kasashen waje da kuma jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali, sakamakon tabarbarewar farashin man a duniya. Matatar Man Dangote da ke yankin Lekki na jihar Legas, ana sa ran za ta sauya wannan lamari ta hanyar karfin tace ganga 650,000 a kowace rana, wadanda suka hada da man fetur da dizal da man jiragen sama, da sauran su. Haka kuma, matatar Man za ta samar da damarmaki iri-iri ga ma’aikata na cikin gida, inda ake sa ra

Gwamnatin Nigeria Zata Daina Ciyar Da Fursunonin Jihohi Daga Karshen Wannaann Shekara

Image
Gwamnatin tarayya a Najeriya ta ce za ta daina ciyar da fursunonin jihohi da ke tsare a gidajen yarin ƙasarnan daga ƙarshen wannan shekara. A wata sanarwa da Ministan Harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya fitar ya ce matakin, zai fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2023. Ministan ya ce mutanen da suka aikata laifi a jihohi ne fiye da kashi 90% na ɗaurarrun da ke gidajen yarin Najeriya a yanzu adon haka Jahohi za su fara yin kasafin kuɗi don ciyar da ɗaurarrunsu da ke gidajen yarin tarayya a daidai lokacin da gwamnatin Tarayya ta ke  jiran su gina gidajen yari na kansu. Tuni kundin tsarin mulkin Nigeria ya cire ikon kula da gidajen yari daga hannun gwamnatin Tarayya kadai tun bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu akai. Shin yaya ku ka dubi wannan mataki? Shin ko hakan zai kara Inganta tsarin kula da walwalar gidajen Gyaran hali a Nigeria? Za mu karanto wasu daga cikin ra'ayoyinku a labaranmu da yardar Allah sai mun ji daga gare ku....

Cikin Fotuna Wani Matashi Ya Fara Tattaki Daga Katsina Zuwa Abuja Domin Taya Tinubu Murnar Lashe Za6e

Image
Matashi Mai shekaru 21 ya doshi hanyarsa ta yin tattaki daga jihar Katsina zuwa Abuja domin taya murna ga zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Asiwaju Ahmad Tinubu A yayin tattauna da Matashin mai suna Abdula'aziz Abdullahi Mashi, da ya fito a ƙaramar hukumar Mashi a garin 'Yar riga, yace ya ƙudiri aniyar yin tattakin ne don nuna ƙauna ga Asiwaju Ahmad Tinubu. Ya zuwa yanzu, Matashin ya kama hanyar tattaki daga jihar Katsina zuwa Abuja domin taya zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Asiwaju Ahmad Tinubu murnar rantsar da shi a matsayin Shugaban Ƙasa a ranar 29 ga Watan Mayu. Kafin Matashin ya fara dosar hanyar sa ta yin tattakin, shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Mashi da kuma shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina baki ɗaya, yace da sanin su ne ya fara gudanar da tattakin. Katsina Post ta tawaito cewa, Matashi mai suna Abdula'aziz Abdullahi Mashi, wanda shakarun sa da ba za su wuce 21 a duniya ba, ya zuwa yanzu yayi nisa a tattakin da ya fara gudanar wa tin da safiyar yau Juma'a.

TARIHIN SHUGABAN KASA MAI BARIN GADO MUHAMMAD BUHARI GCFR

Image
Tarihin Janaral Muhammadu Buhari, GCFR A Daure A Karanta 👂 Shimfida Manjo Janar Muhammadu Buhari, sojan Najeriya mai ritaya, sannan kuma ɗan siyasa. Jajirtaccen mutum wanda ‘yan Najeriya suke yiwa laƙabi da “Mai Gaskiya”. Wannan kalma ta ‘yan Najeriya ta tabbata a kansa saboda kasantuwarsa maras hannu a cikin badaƙalolin maƙudan kuɗaɗen da mafiya yawa daga tsoffi da sabbin shugabannin Najeriya suka tsunduma kawukansu a ciki. Janaral Muhammadu Buhari mutum ne da ke da gogayya a fannin mulki saboda aikin da ya yi a gidan soja, wanda ya fara tun daga sakan laftanar har sai da ya zamo shugaban ƙasa bayan tarin muƙaman da ya riƙe kafin hakan, sannan kuma bayan ritayar sa ya shiga siyasa wacce ta sake bashi damar sake ɗarewa kujerar shugabancin Najeriya a karo na biyu kuma a matsayin farar hula. Ya samu kafa tarihin cewa shi ne farkon Ɗan’najeriya da ya taɓa tsayawa takarar zaɓe a jama’iyyar hamayya sannan kuma ya kayar da shugaban da ke kan karagar mulki. Haihuwarsa Janaral Muhammadu Buhar

"Yan Ta'adda Sun Kashe Sama Da Mutum 200 A Jihar Zamfara A Jiya Jummuat INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN

Image
Cikin Fotuna Kadan Daga Cikin Mutanen Da Yan Ta'adda Jihar zamafara sukq Kashe A Wasu Kauyukan Jihar Zamfara kenan muna Rokon Allah Subhanahu Wata aka Daya Karbi djahadarsu ya jikan su Allah ya Mana Maganin Matsalar tsaro

Yadda Zaka Sayi Data Na Naira 200 Da Naira Hamsin Dinka Sayen Data Mai Sauki

Image
Yadda zakayi Da farko Shine Zaka saka *131*25# Lallai Wannnn Data Mai Sauki ce

Sabbin Hotunan Jarumar Kannywood Maryam Yahaya Bayan Ta Dan Samu Sauki

Image