Cikin Fotuna Wani Matashi Ya Fara Tattaki Daga Katsina Zuwa Abuja Domin Taya Tinubu Murnar Lashe Za6e
Matashi Mai shekaru 21 ya doshi hanyarsa ta yin tattaki daga jihar Katsina zuwa Abuja domin taya murna ga zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Asiwaju Ahmad Tinubu
A yayin tattauna da Matashin mai suna Abdula'aziz Abdullahi Mashi, da ya fito a ƙaramar hukumar Mashi a garin 'Yar riga, yace ya ƙudiri aniyar yin tattakin ne don nuna ƙauna ga Asiwaju Ahmad Tinubu.
Ya zuwa yanzu, Matashin ya kama hanyar tattaki daga jihar Katsina zuwa Abuja domin taya zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Asiwaju Ahmad Tinubu murnar rantsar da shi a matsayin Shugaban Ƙasa a ranar 29 ga Watan Mayu.
Kafin Matashin ya fara dosar hanyar sa ta yin tattakin, shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Mashi da kuma shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina baki ɗaya, yace da sanin su ne ya fara gudanar da tattakin.
Comments
Post a Comment