TARIHIN SHUGABAN KASA MAI BARIN GADO MUHAMMAD BUHARI GCFR
Tarihin Janaral Muhammadu Buhari, GCFR
A Daure A Karanta 👂
Shimfida
Manjo Janar Muhammadu Buhari, sojan Najeriya mai ritaya, sannan kuma É—an siyasa. Jajirtaccen mutum wanda ‘yan Najeriya suke yiwa laÆ™abi da “Mai Gaskiya”. Wannan kalma ta ‘yan Najeriya ta tabbata a kansa saboda kasantuwarsa maras hannu a cikin badaÆ™alolin maÆ™udan kuÉ—aÉ—en da mafiya yawa daga tsoffi da sabbin shugabannin Najeriya suka tsunduma kawukansu a ciki.
Janaral Muhammadu Buhari mutum ne da ke da gogayya a fannin mulki saboda aikin da ya yi a gidan soja, wanda ya fara tun daga sakan laftanar har sai da ya zamo shugaban ƙasa bayan tarin muƙaman da ya riƙe kafin hakan, sannan kuma bayan ritayar sa ya shiga siyasa wacce ta sake bashi damar sake ɗarewa kujerar shugabancin Najeriya a karo na biyu kuma a matsayin farar hula.
Ya samu kafa tarihin cewa shi ne farkon ÆŠan’najeriya da ya taÉ“a tsayawa takarar zaÉ“e a jama’iyyar hamayya sannan kuma ya kayar da shugaban da ke kan karagar mulki.
Haihuwarsa
Janaral Muhammadu Buhari, haifaffen garin Daura ne ta cikin Jahar Katsina. An haife shi a ranar 17 ga watan Disamba na shekarar 1942. Sunan mahaifinsa Adamu, mahaifiyarsa kuma Zulaihatu. Mahaifinsa ya rasu a lokacin da Janar Muhammadu Buhari ya ke da shekara huÉ—u kacal a duniya.
Karatunsa
Manjo Janaral Muhammadu Buhari ya yi karatunsa na firamare a garin Daura da kuma Mai’adua daga shekarar 1948 zuwa 1952. Daga nan sai ya shige makarantar Middle ta Katsina a shekarar 1953. Sannan kuma sai ‘Katsina Provincial School’ wacce daga baya ta koma Kwalejin Gwamnati ta Katsina, daga shekarar 1956 har zuwa 1961.
A shekarar 1961, Manjo Janaral Muhammadu Buhari ya samu shiga makarantar sojojin Najeriya da ke Kaduna (Nigerian Military Training School, Kaduna), inda ya gama a shekarar 1963.
Bayan kammala wancan horo da ya samu na soja a Kaduna, a cikin wannan shekara ta 1963 aka tura shi Æ™aro karatu a Æ™asar Ingila inda ya samu horo a makarantar ‘Cadet School’ da ke garin Aldershot ta Æ™asar Ingila. Da Kammalawarsa kuma nan take aka Æ™addamar da shi a matsayin sakan laftanar (second lieutenant) na soja. Aka kuma tura shi zuwa Abekuta.
A dai wannan shekarar ta 1963 aka sake tura shi samun Æ™arin horo a fanni ‘Platoon Commanders Course’ wanda ya halarta a makarantar sojojin Najeriya ta Kaduna (Nigerian Military College, Kaduna), makarantar da ya fara da ita. Ya samu wannan horo har zuwa 1964.
A shekarar 1965, Manjo Janaral Muhammadu Buhari ya sake tafiya samun horo a fannin ‘Mechanical Transport Officers Course’, wanda ya yi a makarantar ‘Army Mechanical Transport School’ da ke garin Borden, na Æ™asar Ingila.
Sannan kuma a shekarar 1973 ya sake samun horo makarantar ‘Defence Services’ Staff College’, da ke garin Wellington na Æ™asar Indiya. A shekarar 1979 zuwa 1980 kuma ya je kwalejin yaÆ™i ta sojoji (United States Army War College) da ke Æ™asar Amurka.
Muƙaman da ya Riƙe
Manjo Janaral Muhammadu Buhari, ya riƙe muƙamai da dama tun fitowarsa ta farko daga makarantar soja da aka fara ƙaddamar da shi a matsayin sakan laftanar (second lieutenant). Manya daga cikin muƙaman da ya riƙe sun haɗa da:
1, Gwamnan Jahar Arewa-maso-Gabas Najeriya a shekarar 1975, a zamanin mulkin shugaban Najeriya Janaral Murtala.
2, Kwamishinan man fetur na tarayyar Najeriya (Federal Commissioner for Petroleum Resources) muƙamin da ya ke daidai da na minister a yanzu, daga shekarar 1976 zuwa 1978.
3, Ya riƙe wannan muƙami a zamanin mulkin soja na shugaba Janaral Olushegun Obasanjo.
4, Ciyaman na Kamfanin Manfetur na Najeriya (Chairman, NNPC) a shekarar 1978.
5, Shugaban rundunar sojojin Najeriya ta uku da ke Jos (General Officer Commanding (GOC), Third Armored Division of Jos) a shekarar 1983.
6, Shugaban ƙasa. Manjo Janara Muhammadu Buhari ya zama shugaban mulkin soja na tarayyar Najeriya a shekarar 1984 har zuwa 1985 bayan an hamɓarar da gwamnatin farar hula ta shugaba Shehu Usman Shagari.
7, Shugaban hukumar tara rarar manfetur (Chairman of Petroleum Trust Fund (PTF), daga 1995 zuwa 99 muƙamin da ya riƙe lokacin yana farar hula a zamanin mulkin shugaban soja na Najeriya marigayi Janaral Muhammadu sani Abacha
Shigarsa Siyasa
A shekarar 2003, Janaral Muhammadu Buhari ya shiga siyasa Æ™arÆ™ashin tutar jama’iyyar ANPP, jama'iyyar da ta bashi takarar shugaban Æ™asa wanda ya shiga zaÉ“e tare da shugaba Janaral Olushegun Obasanjo mai ritaya.
Takarkarun da ya yi
Janaral Muhammadu Buhari ya tsaya takarar neman É—arewa kujerar shugabancin Najeriya a karo na biyu a matsayin farar hula har sau huÉ—u, sai a karo na huÉ—u ne aka dace. Ga yadda lissafin ya ke:
A shekarar 2003, shugaba Muhammadu Buhari ya yi takara a ƙarƙashin tutar ANPP.
Shekarar 2007, ya sake wata takarar a dai jama’iyyar ANPP.
Shekarar 2011, ya sake yin takara wannan karon kuma a sabuwar jamaiyyarsa ta CPC mai alamar alƙami.
Sai kuma 2015, ya sake yin wata takarar wacce ita ta kai shi ga É—arewa kujerar shugabancin Najeriya a Æ™arÆ™ashin tutar jama’iyyar gamayya ko haÉ—aka ta APC.
Shugaban Farar Hula
An sake rantsar da Janaral Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Najeriya karo na biyu, a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2019, muƙamin da yake kansa har zuwa yau ɗin nan.
Iyali da dangi
Buhari ne É—a na 23 a cikin 'ya'yan mahaifinsa malam Adamu, sa'annan ya tashi a hannun mahaifiyarsa mai suna Zulaihatu bayan rasuwar mahaifinsa yana É—an shekaru 4 a duniya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya auri mata biyu a rayuwarsa. Akwai Safinatu Yusuf wacce ita ce matarsa ta farko da ya aura (daga 1971 zuwa 1988) kuma ta rasu ta bar manyan 'ya'ya kafin ya auri Aisha Halilu a shekarar 1989
'Ya`ya
Muhammad Buhari yana da 'ya'ya guda goma Wanda suka haÉ—a da:
Zulaihat (marigayiya)
Fatima
Musa (marigayi)
Hadiza
Safinatu
Aisha
Halima
Yusuf
Zarah
Amina
Karin Bayani.
Tsohon Sojan, Dogo, Siriri, wanda aka haifa a garin Daura mai cike da tarihi da ke arewacin Nijeriya, shekaru 73 da suka wuce, ya yi suna ne a shekarar 1983, a lokacin da ya hambarar da zababbiyar gwamnatin farar hulla.
A matsayinsa na soja mai mulkin kama-karya a lokacin, ya zama mutumin da ke nuna ba-sani-ba sabo wajen yaki da cin hanci da rashawa, inda ya kulle ‘yan siyasa masu yawa da ake zargi da cin hanci da rashawa.
Tuni dai Muhammadu Buhari ya bayyana kansa cewar yanzu shi ma ya rungumi dimokuradiyya.
Ya samu nasara ne tare da gagarumin rinjaye a zaben da masu sa ido suka ce shi ne ya fi kowanne inganci wajen nuna adalci a kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika.
Comments
Post a Comment