Gwamnatin Nigeria Zata Daina Ciyar Da Fursunonin Jihohi Daga Karshen Wannaann Shekara

Gwamnatin tarayya a Najeriya ta ce za ta daina ciyar da fursunonin jihohi da ke tsare a gidajen yarin ƙasarnan daga ƙarshen wannan shekara.

A wata sanarwa da Ministan Harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya fitar ya ce matakin, zai fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2023.

Ministan ya ce mutanen da suka aikata laifi a jihohi ne fiye da kashi 90% na ɗaurarrun da ke gidajen yarin Najeriya a yanzu adon haka Jahohi za su fara yin kasafin kuɗi don ciyar da ɗaurarrunsu da ke gidajen yarin tarayya a daidai lokacin da gwamnatin Tarayya ta ke  jiran su gina gidajen yari na kansu.

Tuni kundin tsarin mulkin Nigeria ya cire ikon kula da gidajen yari daga hannun gwamnatin Tarayya kadai tun bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu akai.
Shin yaya ku ka dubi wannan mataki?

Shin ko hakan zai kara Inganta tsarin kula da walwalar gidajen Gyaran hali a Nigeria?
Za mu karanto wasu daga cikin ra'ayoyinku a labaranmu da yardar Allah sai mun ji daga gare ku....

Comments

Popular posts from this blog

Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Babbbar Matatar Mai Ta Dangote A Lagos