Popular posts from this blog
Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Babbbar Matatar Mai Ta Dangote A Lagos
Shugaba Muhammadu Buhari Zai Kaddamar Da Babbar Matatar Mai Ta Dangote A Legas Ana sa ran fara aikin wannan matatar Mai zai haifar da gagarumin tasiri ga tattalin arzikin Najeriya da kuma rayuwar 'yan kasar. A halin yanzu dai Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke da arzikin Man Fetur a nahiyar Afirka, amma duk da haka ta dogara kacokan kan shigo da taceccen mai daga kasashen waje domin biyan bukatunta na cikin gida. Kasar dai na kokawa da kalubalen rashin isassun kayan aikin tace mai a cikin gida, lamarin da ya janyo raguwar kudaden da take samu daga kasashen waje da kuma jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali, sakamakon tabarbarewar farashin man a duniya. Matatar Man Dangote da ke yankin Lekki na jihar Legas, ana sa ran za ta sauya wannan lamari ta hanyar karfin tace ganga 650,000 a kowace rana, wadanda suka hada da man fetur da dizal da man jiragen sama, da sauran su. Haka kuma, matatar Man za ta samar da damarmaki iri-iri ga ma’aikata na cikin gida, inda ake sa ra...
Comments
Post a Comment