Masu Zanga Zanga Sun Tare Hanya A Jihar Bauchin Nigera

DA DUMI DUMIMSA

Rahotannin da Suke Fitowa Daga Garin Bauchi Sunnuna Wasu daga chikin mazauna unguwar birshin fulani, dake cikin garin bauchi sun tare wata hanya wacce daga bauchi tatafi Dass,

Suntare wannan hanyane da niyyar yin zanga-zangar matsalar tsaro da take addabar su a yankin.

Zuwa yanzu masu ababan hawa sunfara korafi ga gwamnati domin tare musu hanyar da mutanen sukayi sunhada dandazon jama'a masu abun hawan jibge akan hanyar.

Wakilinmu ya samu zantawa da daya daga chikin masu zaga zanzgan wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidamasa cewar "yau wajen makonni biyu kenan da faruwar kai harin yan bindiga yankin inda har suka kashe mutum biyu ciki harda wani babban ma'aikacin kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar bauchin ( Malam Abubakar Muhammad)".

Yakara da cewa " kafin hakama anyi garkuwa da wasu mutane sa'annan kuma sai wannan harin na yan bindiga ya biyo baya wannan shine dalilin dayasa suke wannan zanga-zanga.

Naeem Sabeet Master 

Comments

Popular posts from this blog

TARIHIN SHUGABAN KASA MAI BARIN GADO MUHAMMAD BUHARI GCFR

Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Babbbar Matatar Mai Ta Dangote A Lagos