Aliyu Dahiru Aliyu : Nasha Mamaki Da Naji Abdullahi Gadon Kaya Yana Kazafi Prof Maqari Yana Bawa Masu zagin Annabi SAW KARIYA
Haduwata ta biyu da Mallam Maqari maganar da ya yi min ita ce ta yaya za a yi bincike (research) domin a yi maganin matsalar yan haqiqa a cikin sufanci. Don haka na cika matuka da mamaki da Mallam Abdullahi ya ce yana da “audio” din kiransa wai yana nemawa masu zagin Allah da Annabi mafaka. Har yanzu ban dena mamaki ba! Kai har da muka taba zuwa gurinsa da Adamu Tilde a Abuja sai da ya yi magana makamanciyar hanyoyin dakile guluwwi a sufanci wanda masu yinsa sun dauko fahimtarsu ne a falsafofin addinin Hindu maimakon falsafa da tauhidin musulinci. Allah ya yaye mana hassada ya kuma hanemu da yin karya.
Comments
Post a Comment