Ya Zama Wajibi Iyaye Su Cire Kunya Subawa Yaransu Tarbiyya Da Kunne Na Naji

A kunne na wata mata k'abila ce zata ajiye 'yarta a Makaranta, sai ta ke gaya mata da turanci "Kada ki kuskura ki bari wani ya bude miki dan kamfai (pant), duk wanda ya taba miki ki gayawa Malamarku ko kiyi ihu" wannan wasiyyar ta ratsa ni matuk'a. A raina nace, Ashe k'abilu ma sun damu da batun tarbiyya! 

Yanzu fa al'amura sun lalace, kana ganin 'yarka karama ce, ai Primary ne, kana jin ba abinda zai faru, a haka kuma abubuwa suke faruwa yara suyi shiru suki magana. Ya zama dole iyaye su kau da kunya su dinga gayawa yara gaskiyar lamari, domin gina musu tarbiyya mai kyau.

Zamani ya rikice, abinda baka taba zaton zai faru ba sai kaji yana faruwa. Yara amana ce, iyaye suyi iyakar kokarinsu ba tare da boye boye ba wajen baiwa 'ya 'yansu ingantacciyar tarbiyya, domin a samu al'umma ta gari. Allah ya shirya mu shirin addini, ya kuma kare mu daga sharrin rudin wannan zamanin. Amin.

Yasir Ramadan Gwale
01-07-2021

Comments

Popular posts from this blog

TARIHIN SHUGABAN KASA MAI BARIN GADO MUHAMMAD BUHARI GCFR

Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Babbbar Matatar Mai Ta Dangote A Lagos