TARIHIN SHUGABAN KASA MAI BARIN GADO MUHAMMAD BUHARI GCFR
Tarihin Janaral Muhammadu Buhari, GCFR A Daure A Karanta 👂 Shimfida Manjo Janar Muhammadu Buhari, sojan Najeriya mai ritaya, sannan kuma ɗan siyasa. Jajirtaccen mutum wanda ‘yan Najeriya suke yiwa laƙabi da “Mai Gaskiya”. Wannan kalma ta ‘yan Najeriya ta tabbata a kansa saboda kasantuwarsa maras hannu a cikin badaƙalolin maƙudan kuɗaɗen da mafiya yawa daga tsoffi da sabbin shugabannin Najeriya suka tsunduma kawukansu a ciki. Janaral Muhammadu Buhari mutum ne da ke da gogayya a fannin mulki saboda aikin da ya yi a gidan soja, wanda ya fara tun daga sakan laftanar har sai da ya zamo shugaban ƙasa bayan tarin muƙaman da ya riƙe kafin hakan, sannan kuma bayan ritayar sa ya shiga siyasa wacce ta sake bashi damar sake ɗarewa kujerar shugabancin Najeriya a karo na biyu kuma a matsayin farar hula. Ya samu kafa tarihin cewa shi ne farkon Ɗan’najeriya da ya taɓa tsayawa takarar zaɓe a jama’iyyar hamayya sannan kuma ya kayar da shugaban da ke kan karagar mulki. Haihuwarsa Janaral Muhammadu Buhar...
Comments
Post a Comment